News
Jami’an Tsaro A Indiya Sun Kama Wata ‘Yar Najeriya Bisa Zargin Safarar Hodar Iblis Da Takai Gram 121 A Cikin Burodi
’yan sanda sun kama wata ’yar Najeriya mai shekaru 29, Olajide Esther Iyanuoluwa, bisa zargin safarar hodar iblis da ta boye a cikin Burodi.
Hukumomin tsaro a birnin Bengaluru sun ce sun cafke wadda ake zargin ne yayin da take tafiya a wata bas daga Mumbai zuwa Bengaluru, bayan samun bayanan sirri game da motsinta.
Jami’an EFCC Sun Bankado Wasu Kadarori Na Kimanin N212bn Da Ke Da Alaka Da Malami
Jaridar PUNCH ta ruwaito a ranar Talata cewa ‘yan sanda sun ƙwace hodar iblis din da darajarta takai kimanin rufi miliyan 12 (miliyan 194,079,600 kenan a kudin Najeriya) daga hannun wadda ake zargin, lamarin da ke nuna yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙara amfani da abinci na yau da kullum wajen jigilar kwayoyi.
An bayyana sunan wadda ake zargin da Olajide Esther Iyanuoluwa. Ta je New Delhi a bara da takardar karatu (student visa), amma bincike ya nuna cewa ba ta taɓa yin rajista a kowace makaranta ba.
Maimakon haka, rahotanni sun sheda cewa tana yawan sauya matsuguni a birnin Mumbai da kewaye, ciki har da Ghatkopar (Gala Nagar), Ambawadi da Nallasopara, inda ake zargin tana aikata safarar miyagun ƙwayoyi.
