Connect with us

News

JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar UTME Da Aka Yi A Ranakun Juma’a Da Asabar

Published

on

jamb exam1 (1)

Hukumar haɗaka ta kula da lamuran samar da gurbin karatu a manyan makarantu ga ɗalibai (JAMB), ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarrabawar UTME a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu.

A wata sanarwa da Kakakin JAMB, Fabian Benjamin ya fitar wa manema labarai a yau Lahadi, hukumar ta bayyana cewa sakamakon ɗalibai guda 1,264,940 ne da suka rubuta a kwana biyun aka sako.

Advertisement

Wasu Na Ɗaukar Nauyin Ta’addanci Domin Cim Ma Muradun Siyasa  — Ministan Tsaron Nijeriya

Haka kuma, hukumar ta tunatar da cewa ta fitar da wanda aka yi a ranar Alhamis.

Advertisement

Da fari, JAMB ta fitar da sakamakon ɗalibai 632,752 da suka yi a ranar Alhamis, wato 16 ga Afrilu, 2026, wanda ya kai jimillar adadin na waɗanda aka fitar zuwa guda 1,897,692 a yanzu.

JAMB ta shawarci ɗaliban da al’amarin ya shafa da su duba sakamakonsu ta sahihin hanyoyin saƙonnin kar ta kwana (SMS) ta hanyar aika UTMERESULT zuwa 55019 or 66019 da lambar wayar da suka yi rajistar jarrabawar da ita.

Advertisement

A cewar hukumar, sakamakon da aka fitar zuwa yanzu na duka kwanaki ukun ne da aka shafe ana gudanar da ayyukan rubuta jarrabawar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending