News
An Yanke Wa Matar Da Aka Kama Tana Kai Wa ’Yan Bindiga Alburusai Hukuncin Kisa A Katsina
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Katsina ta yanke wa wata mata mai suna Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin haɗa baki da kuma taimaka wa ayyukan ta’addanci.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Hauwa’u ne a ranar 16 ga Satumbar 2023 a tashar mota ta Jibia, yayin da take ƙoƙarin kai wa wani jagoran ’yan bindiga alburusai, lamarin da ya janyo fara shari’arta a gaban kotu.
Gwamnatin Katsina Ta Haramta Sana’ar POS, Bunburutu Da Cajin Waya
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a A.B. Bawale ya ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da suka tabbatar da cewa wadda ake tuhuma ta aikata laifukan da ake zarginta da su.
Alƙalin ya bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, wanda hakan ya sa aka same ta da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Bisa haka, kotun ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya kamar yadda dokokin hukunta laifuffuka suka tanada kan masu hannu a ayyukan ta’addanci da tallafa wa masu aikata su.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro da na shari’a ke ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan masu hannu wajen taimaka wa ƙungiyoyin ’yan bindiga da sauran masu aikata laifukan ta’addanci a sassan ƙasar nan.
