News
Kotu Ta Daure Wata Mata Shekara 10 Kan Safarar Makamai Ga ’Yan Bindiga A Kano
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wata mata mai suna Raya Haruna hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari bisa samunta da laifin safarar makamai da harsasai ga ‘yan bindiga da ke aiki a wasu sassan Arewacin Najeriya.
Alkalin kotun mai shari’a Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan samun wanda ake tuhuma da laifuka uku da su ka shafi safarar makamai ba bisa ka’ida ba dakuma bayar da tallafin kayan aiki ga masu aikata laifuka.
Iran Ta Sake Rufe Mashigin Hormuz Bayan Harin Isra’ila A Lebanon
jami’an tsaro sun gabatar da tuhume-tuhumen ne a karkashin Dokar Makamai da kuma Dokar Yaki da Ta’addanci ta 2022, wanda ke haramta mallaka, samar da makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma bayar da tallafi ko taimako ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu alaka da aikata laifuka.
Jami’an tsaro sun kama wadda aka yanke wa hukuncin ne a shekarar 2024 a yayin wani sumame da su ka yi da nufin dakile safarar makamai zuwa ga ‘yan fashi da ke addabar al’umma a sassan jihar Kano da makwabta.
Tun bayan kama ta, mai laifin ta kasance a tsare a gidan gyaran hali, ya yin da take fuskantar shari’a a gaban babbar kotun tarayya bisa zargin da ake da alaka da safarar makamai da harsasai ga kungiyoyin masu laifi.
Da ya ke yanke hukunci, Mai shari’a Amobeda ya ce safarar makamai da harsasai wata babbar hanyar alaka ce a cikin jerin ayyukan ta’addanci, wadda ke bai’wa kungiyoyin masu laifi damar kai hare-hare da ke haifar da rasa rayuka, jikkata, da kuma aikata barna mai yawa.
Mai shari’a Amobeda ya kara da cewa, a karkashin Dokar Yaki da Ta’addanci ta 2022, samar da kayan aiki, sufuri, ko kowane irin tallafi da ke saukaka ayyukan ta’addanci babban laifi ne da doka ta tanadi hukunci a kansa.
Daga nan ne kotun ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ba tare da zabin tarar kowanne daga cikin tuhume-tuhumen guda uku da ake yi mata ba, tare da zartar da hukuncin daurin rai-da-rai daga ranar da aka kama ta da kuma tsare ta a shekarar 2024.
Mai shari’a Amobeda ya kuma bayar da umarnin mika makaman da harsasan da aka kwato ga Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, tare da bayar da umarnin shigar da wadda aka yanke wa hukunci cikin shirye-shiryen gyaran hali da tarbiyya ya yin da take gidan yari.
