Connect with us

Uncategorized

Mutum Miliyan 2 Na Ɗauke Da Cutar Hanta (Hepatitis) A Kano — KSACA

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Yadudu Waqf Foundation sun gudanar da gwajin cutar hanta (Hepatitis) kyauta ga al’umma a harabar Jami’ar Bayero da ke Kano, a wani ɓangare na bikin ranar cutar Hepatitis ta duniya.

A yayin taron, gwamnatin jihar ta yi kira ga masu sana’ar aski da masu yankan farce da su riƙa tsaftace kayayyakin aikinsu yadda ya kamata domin dakile yaɗuwar cutar. Haka kuma ta shawarci jama’a su mallaki nasu kayan aski da na yankan farce domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Jami’an NDLEA Sun Kama Hodar Iblis Da A Ka Boye A Cikin Turmi Za A Kai China

Shugaban Hukumar Yaki da Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), Dakta Usman Bashir, ne ya bayyana hakan yayin taron da hukumar ta shirya tare da haɗin gwiwar Yadudu Waqf Foundation.

Ya ce kimanin mutum miliyan biyu ne ake hasashen suna ɗauke da cutar Hepatitis a Jihar Kano, inda ya ƙara da cewa mata ne suka fi yawa a cikin masu fama da cutar.

Dakta Usman Bashir ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da kayan gwaji da magunguna ga mata masu juna biyu, tare da yi wa jariran da suka haifa rigakafin Hepatitis domin kare su daga kamuwa da cutar tun daga haihuwa.

Advertisement

Ya ce cutar Hepatitis na yaɗuwa ta hanyar jini, yawu da kuma saduwar jima’i, don haka ya buƙaci jama’a su guji amfani da kayan aski da na yankan farce na wasu ba tare da tabbatar da an tsaftace su ba. Ya kuma jaddada cewa yin gwajin cutar da wuri na taimakawa wajen gano ta da kuma hana ci gaba da yaɗuwarta.

Da yake zantawa da wakilinmu, Bashir Faruk Durumin Iya, wakilin Gidauniyar Yadudu Waqf Foundation, Dakta Muhammad Yadudu, ya bayyana cewa an kafa gidauniyar ne bayan rasuwar Captain Isma’il Yadudu sakamakon cutar Hepatitis.

Ya ce manufar gidauniyar ita ce wayar da kan al’umma, samar da gwaje-gwaje kyauta da kuma tallafa wa masu fama da cutar domin rage yaɗuwarta da kuma ceton rayuka.

 

 

Arewa Radio 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending