Connect with us

News

Sarkin Funakaye Da Ke Jihar Gombe Ya Rasu

Published

on

Marigayi Sarkin Funakaye, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga rasuwa sakamakon bugun zuciya.

Advertisement

Sarkin na Funakaye, ya rasu ne a daren Asabar da misalin karfe 12:00 na dare.

Har Yanzu Akwai Makarantun Sakandare 75 Da Ke Rufe A Zamfara

Advertisement

Kafin rasuwarsa, marigayin ko a ranar Asabar ya halarci taron da Ministan Sadarwar, Isa Ali Ibrahim Pantami ya gudanar a Otel din Custodian da ke Gombe, kafin ya koma garin sa na Bajoga da misalin karfe 2:30 na rana

Marigayin ya zama Sarkin Funakaye ne bayan rasuwar yayansa, Alhaji Muhammad Kwairanga Abubakar, aka nada shi a ranar shida ga watan Fabarairun 2021, lokacin shi ne Dan Majen Funakaye

Advertisement

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na ranar Lahadi a fadarsa da ke garin Bajoga hedkwatar karamar hukumar ta Funakaye.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILLY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending