Connect with us

News

PDP ta zargi Tinubu da yin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, ya bukaci a kama dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da karkatar da halasta kudaden haramun a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas.

 

Advertisement

Kwamitin ya yi kira ga Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, (NDLEA) da Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Kasa Zagon Kasa (EFCC) da su gaggauta cafke Tinubu tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.

 

Advertisement

Yau ne Ronaldo zai fara buga wasa a mungiyar Al-Nassr

PDP ta yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja a ranar Lahadi.

 

Advertisement

Aminiya ta rawaito cewa Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben, Mista Daniel Bwala, ya bukaci NDLEA da ta gayyaci Tinubu domin yi masa tambayoyi kan wata badakalar Dala 460,000 da ya yi tsawon shekaru a kasar Amurka.

 

Advertisement

Bwala, wanda ya kuma yi Allah wadai da kwamitin da Tinubu ya kafa, wanda ya bayyana shi a matsayin ‘yan bindiga, ya bukaci hukumomin tsaro da su kama su sannan su gurfanar da duk wanda ke cikin kwamitin da ake kira da ‘Jagaban Army’.

 

Advertisement

Ya kara da cewa ‘yan adawa da dama na fuskantar barazana gabanin zaben da ake shirin shiga.

 

Advertisement

Wani mai magana da yawun kamfen na PDP, Phrank Shaibu, ya yi zargin cewa har yanzu Tinubu na ci gaba da gudanar da kasuwancin haramtattun kwayoyi tun daga 2015 zuwa yanzu.

 

Advertisement

Ya kara da cewa, Tinubu ya aike Dalar Amurka miliyan 4.3 zuwa wani kamfani da ke Kasar Colombiya.

 

Advertisement

A satin da ya gabata ne dai, mai magana da yawun kwamitin yakin zaben APC, Festus Keyamo, ya aike wa EFCC da ICPC takarda kan bukatar su cafke Atiku.

 

Advertisement

Keyamo ya zargi Atiku da hannu wajen gudanar da wasu harkalloli da suka yi sama da fadi da dukiyar jama’a a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasa.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending