Politics
Dalilan Da Ya Sa Shugaban Jamiyyar APC Na Kasa Ya Yi Murabus
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar murabus dinsa a daren jiya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a watan Maris din shekarar 2022, ya aike da takardar murabus dinsa zuwa fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja gabanin dawowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu daga taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) da ake gudanarwa a Kenya.
SUDAN:Ana ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na kasar Sudan
Adamu tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya aika wasikar murabus din ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
“Ya yi murabus. An aika da takardar murabus din da ya sanya wa hannu zuwa fadar Shugaban Kasa Villa. Wasikar an aika wa shugaba Tinubu. Amma tun da shugaban kasar ya tafi Kenya don halartar taron kungiyar AU, an aike da wasikar zuwa ga shugaban ma’aikatansa,” inji majiyar.
Hakazalika, wata majiya ta kusa da Adamu ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa, “Shugaban Jamiyyar na Kasa ya yi murabus ne biyo bayan gungun jama’a da ke kusa da shugaban kasar da suke shirin kunyata shi a taron jam’iyyar da za a yi gobe da Laraba.”
Sai dai majiyar ta musanta wani rahoto da ke cewa shugaba Tinubu ne ya bukaci Adamu ya yi murabus gabanin taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na kasa da za a yi gobe da Laraba.
Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 10 da 11 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan kwamitin ta na kasa da na NEC domin warware matsalolin da suka shafe ta da kuma rikicin da ke tsakanin kwamitin ayyuka na kasa (NWC).
