Connect with us

Politics

Jam’iyyar APC ta amince da Ganduje, Basiru a matsayin shugaban jam’iyyr da kuma  sakatare.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

A jiya ne dai ake sa ran kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC zai amince da zaben Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da kuma Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa a taron na gaba.

Matakin dai ya biyo bayan zabin mutanen biyu ne, bayan ficewar tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu da sakatare, Sanata Iyiola Omisore.

Advertisement

Ana sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tabbatar da ranar taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC bisa bukatar NWC.

Dalilan Da Ya Sa Shugaban Jamiyyar APC Na Kasa Ya Yi Murabus

Har ila yau, NWC, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC da gwamnonin sun amince da cewa, ya kamata a samu sauyi cikin kwanciyar hankali da kuma ci gaba da tsarin shiyya-shiyya da aka dade ana yi na kasancewar shugabannin jam’iyyar.

Advertisement

Cool fm ta rawaito cewa wata majiya ta ce kungiyar gwamnonin Progressives’ Forum (PGF) karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, sun gana a Imo State Lodge, Abuja inda suka amince da Ganduje da Basiru.

Kwana daya bayan haka gwamnoni da sauran shugabannin jam’iyyar musamman ‘yan majalisar tarayya sun yi taro da Ganduje da Basiru.

Advertisement

A cewar majiyar, ana sa ran kungiyar ta kasa, wadda shugaba Tinubu yake cikinta, za ta mika wa hukumar zabe hukuncin da gwamnonin APC da sauran kusoshin jam’iyyar suka yanke kafin sabon shugaban da sakatare su karbi ragamar mulki bayan amincewa da zaben.

Tuni kuma an sanar da hukunce-hukuncen ga sassan jahohi da kuma kusoshin majalisar.

Advertisement

Ko da yake ana sa ran babban taron jam’iyyar APC na kasa ne ya amince da sunayen mutanen biyu, amma kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya baiwa hukumar zabe ikon yin aiki a madadin taron a cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending