Connect with us

News

Yadda ƙananan hukumomi 23 ke rayuwa cikin fitinar ‘yan bindiga

Published

on

Yan bindiga

DAGA A YASIR SANI ABDULLAHI.

 

Advertisement

Yayin da ‘yan Najeriya kuka dangane da halin raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita, tun bayan cire tallafin fetur, su kuwa wasu ƙananan hukumomi 23 a jihohin Kebbi, Zamfara da Sokoto, na su raɗaɗin ya zarce na sauran yankunan Arewaci da Kudancin ƙasar nan.

Baya ga tsadar rayuwa da talaucin da ya yi katutu a birane, garuruwa da yankunan karkara, ƙananan hukumomin Isa, Sabon Birni, Gwadabawa, Illela, Tangaza da Goronyo da ke Jihar Sokoto, har sun fara mantawa da abin da ake kira zaman lafiya da kwanciyar hankali. Domin babu ɗayan waɗannan biyun a yankunan su.

Advertisement

Sama Da Mutum Miliyan Daya Suka Yi Gudun Hijira A Arewa Maso Yamma A Nageriya– IOM

A kullum fama su ke yi kan yadda za su tsira, su wayi gari wata safiyar daga hare-haren makasa, mahara, masu garkuwa, ko kuma satar shanu da samamen da suka jefa rayuwar su cikin masifar tashin hankali.

Bincike ya nuna cewa da yawan mazauna yankunan sun yi gudun hijira, wasu sun bada kai, sun yi saranda su rayu a ƙarƙashin ‘yan bindiga, ta hanyar ƙulla yarjejeniya da ‘yan bindiga, ta hanyar riƙa biyan su harajin tilas.

Advertisement

Masu gudu sun gudu sun gudu sun bar gonakin su. Wasu ƙauyukan sun zama kangaye, ba kowa, saboda kowa ya tsere.

Abubakar Bawa, Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnati na sane da irin mawuyacin halin da mazauna yankunan ke ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending