News
DA DUMI-DUMI: Jaridar Inda Ranka Tana Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Babbar Sallah
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanin YAKAM MULTIMEDIA Mai buga Jaridar INDA RANKA da kuma BREAKING NEWS NIGERIA yana taya alummar musulmai murnar bikin babbar sallah ta bana.
Wannan sako na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannu shugaban Muhammad Muhammad zahraddin da Kuma sakataren Kamfanin Yasir Sani Abdullahi
Yanayin Tsadar Rayuwa A Najeriya Ya Yi Tashin Roket Fiye Da Tunanin Mai Tunani.
“Yayin da muka shagala da farin ciki na wannan lokaci muna murna, kamata ya yi kuma mu dage mu tuna da ƴan baya”
“Ɗaya daga cikin ayyuka mafi girma da aka rubuta a tarihi na misali mai kyau akwai sadaukarwar da Annabi Ibrahim ya yi da ɗansa Ismail ga Allah Mahalicci.”
“Hanya mafi kyawu da za mu iya fito da wannan misali, ita ce yin koyi da wannan darasi a wajen al’ummar ƙasarmu da kuma ayyukanmu.”
Ta cikin sakon Muhammad Muhammad zahraddin ya ce, lokacin bikin Babbar sallah lokacine da ya kamata musulmai su Kara nunawa juna kauna da sadakarwa da yafiya da Kara rubanya yin ayyuka don samun kusancin Allah madaukakim sarki, tare yiwa Kasa addur samun zaman lafiya.
Sanarwar ta Kuma bukaci sauran Ma’aikatan da su ci gaba da gudanar ayyukansu bisa tsarin kundin kasa na ‘yan Jarida.
A halin yanzu, ƙasarmu na fama da ƙkalubale iri daban-daban musamman ma taɓarɓarewar tattalin arziƙinmu da kuma taɓarɓarewar tsaro
Muhammad zahraddin Kuma yi kira ga shugabanni da su Kara himma wajen warware wasu daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta kama daga rashin tsaro da Ilimi da lafiya da Kuma bangaren Noma.
