Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa: Akwai Yiwuwar Za’a Fuskanci Matsalar Karancin Abinci A Najeriya  —NEOC

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Najeriya na ci gaba da fama da matsalar karancin abinci, yayin da sabbin bayanai daga cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEOC) suka nuna cewa ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da kadada 115,000 a faɗin Najeriya.

Jihohi 29 da ƙananan hukumomi 154 ne abin ya shafa, inda sama da mutum 611,000 lamarin ya shafa kai tsaye, mutum 225,169 suka rasa matsugunansu, gidaje 83,457 ne suka lalace, mutum 201 ne kuma suka rasa rayukansu sannan mutum 2,119 kuma suka samu raunuka a bana.

Advertisement

Tabbas Nasarar Mutum Tana Samuwa Ne Bayan Juriya Da Hakuri  — HON Baba Mai Duniya 

Jaridar PRNIGERIAN ta ruwaito cewa wannan bayanin na ambaliya ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci da kuma ƙaruwar hauhawar farashin kayan abincin, wanda hukumar kididdiga ta Najeriyan (NBS) ta bayyana ya hau sama da kashi 40 cikin 100.

Wani sabon bincike da babban bankin Najeriya CBN ya gudanar daga ranar 22 zuwa 26 ga Yulin 2024 ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki zai tilastawa magidanta a Najeriya kashe mafi yawan kuɗaɗen shigarsu kan abinci nan da watanni shida masu zuwa.

Al’umma Najeriya dai na cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, tun kafin da kuma bayan darewar shugaba Tinubu, abinda mahukunta a Najeriya ke alakantawa da halin ko in kula da gwamnatin da ta gaba ta yi da tattalin arzikin kasar.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *