News
Yan Bindiga Sun Ƙwace Iko Da Jagorancin Ƙaramar Hukuma A Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin.
“Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga karkashin jagorancin babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. An hana noma daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, an kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu, kiwon lafiya ya durkushe. Mazauna garin suna rokon Gwamna @dikko_radda da gwamnatin tarayya (FG) su kawo musu dauki cikin gaggawa.” in ji sanarwar
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, karamar hukumar Kankara na ci gaba da kasancewa ramin kura, inda hare-haren yankin ya jawo fargaba a fadin kasar, musamman ma sace yara dalibai sama da 300 a watan Disambar 2020.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, gwamnatin jihar Katsina ko hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan rahoton ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
