News
ICPC Ta Gurfanar Da Na Hannun Daman El-rufai A Kotu Kan Zargin Sama Da Faɗi Da Naira Biliyan 311
Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) sun gurfanar da Amadu Sule, Daraktan Kamfanin TMDK Terminal Limited, a gaban kotu kan zargin sama da faɗi da kuɗi har Naira biliyan 311.
LEADSHIP ta ruwaito cewa Sule na da alaƙa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ana tuhumarsa a kan laifuka guda biyar da suka shafi satar kuɗi da kuma riƙe kuɗaɗen da ake zargin na zamba ne, wanda ya saɓa dokar Kuɗi ta 2022.
ICPC ta ce Sule ya mallaki sama da naira biliyan 311 da aka tura ta asusun bankuna kamar Fidelity Bank, Stanbic IBTC da Providus Bank.
An ruwaito cewa kuɗaɗen sun fito ne daga kamfanoni irin su INT Towers Limited, IHS Nigeria Ltd, IHS Towers NG Ltd da Boaz Commodities Limited, domin samar da kayayyakin mai.
Hukumar ta ce Sule “ya kamata ya san” cewa kuɗaɗen haram ne.
Har ila yau, an zarge shi da kamfanin TMDK Terminal Limited da riƙe harajin biliyoyin kuɗaɗe.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Janairu domin sauraron roƙon bayar da belin Sule.
Shari’ar ta jawo hankalin jama’a saboda alaƙar kamfanin TMDK Terminal Limited ke da ita da iyalan El-Rufai.
