News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗin Za A Iya Samun Ɓullar Cutar Sanƙarau A Kano Da Wasu Jihohi 10
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar ɓullar cutar sanƙarau a jihohi 11 na Arewacin Najeriya, ciki har da Jihar Kano, inda ta buƙaci al’umma su ɗauki matakan kariya domin kauce wa kamuwa da cutar.
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya, wato Nigerian Meteorological Agency (NiMet), ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwar kiwon lafiya da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce wasu jihohi na cikin barazanar fuskantar ɓarkewar cutar.
Jami’an NSCDC Sun Kama Matasa 4 Yayin Da Suka Fito Kwacen Wayoyin Masu Zuwa Tahajjud A Kano
Jihohin da ake fargabar za su iya fuskantar cutar sun haɗa da Sokoto State, Zamfara State, Kebbi State, Katsina State, Kano State, Jigawa State, Adamawa State, Gombe State, Bauchi State, Yobe State da Borno State.
NiMet ta bayyana cewa cutar sanƙarau cuta ce mai tsanani da ke shafar ƙwaƙwalwa da lakar baya, wadda ƙwayar cutar Neisseria meningitidis ke haddasawa.
A cewar hukumar, cutar na yaɗuwa ne ta hanyar ɗigon ruwan numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da jama’a suka yi cunkoso ko kuma inda iska ba ta ratsawa yadda ya kamata.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa cutar na iya tsananta cikin sauri, har ma ta zama barazana ga rayuwa idan ba a gano ta da wuri ba ko kuma ba a fara magani cikin gaggawa ba.
“Cutar na iya yin ƙamari cikin sauri kuma tana iya kashe mutum cikin sa’o’i kaɗan idan ba a yi maganinta ba. Sai dai gano cutar da wuri da kuma amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta na taimakawa wajen ƙara damar warkewa da rage illolin da cutar ka iya haifarwa,” in ji NiMet.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu rukunin mutane sun fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar, ciki har da yara da matasa, mutanen da ke rayuwa a wuraren da ake cunkoso, waɗanda ke zaune a yankunan da ke fama da ƙura da bushewar iska, da kuma mutanen da garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi.
Saboda haka, hukumar ta buƙaci mazauna jihohin da abin ya shafa su rika sanya ido kan alamun farko na cutar, waɗanda suka haɗa da zazzaɓi mai zafi farat ɗaya, ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, da amai kamar yanda Jaridar Aminiya ta ruwaito
NiMet ta shawarci duk wanda ya fara ganin irin waɗannan alamun da ya gaggauta zuwa asibiti domin samun kulawar likita cikin lokaci.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
