Connect with us

News

Aƙalla Mutum 7,850 Sun Kamu Da cutar Kwalara A Borno ‎

Published

on

kadugen Kaduna Hospital (1)

Cutar Kwalara ta barke a jihar Borno inda mutum 7,850 sun kamu kuma cutar ta yi ajalin mutum 74.

‎Bisa ga wani bayanai da ma’aikatar lafiya ta fitar ranar 9 ga Yuni ya nuna cewa kungiyar likitoci MSF ta bayyana cewa cutar ya fara barkewa tun a watan Mayu inda daga lokacin zuwa yanzu cutar ta yadu a kauyuka 50 dake kananan hukumomi 14 a jihar.

Advertisement

Majalisar Dattija Ta Yi Amai Ta Lashe Game Da Kiran Kamo Mele Kyari

Mutanen dake dauke da cutar sun yi wa Asibitoci yawa a Jihar Borno.

Advertisement

‎Kungiyar ta ce dole ta kara yawan gadejen kwantar da marasa lafiya na asibitin da suka bude daga gajade 121 zuwa 271 da oda Karin da ake samu na mutanen dake kamuwa da cutar.

‎MSF ta ce ta bude wani asibitin a Dalaram mai fadin gadaje 20 domin rage yawan cinkoson mutanen a asibitocin da suka bude.

Advertisement

‎Zuwa ranar 7 ga Yuni MSF ta ce kwantar da mutum 7,439 da suka kamu da cutar a asibitocin ta biyu da ta bude wanda hakan ke nuna cewa a rana asibitocin na kwantar da mutum 230.

‎Kungiyar ta ce a ranar biyar ga Yuni kungiyar ta samu mutum sama da 500 da suka kamu da cutar amai da gudawa inda kungiyar ta ce wannan shine mafi yawan mutanen da ta samu a rana tun bayan bullowar cutar.

Advertisement

‎Kodinatan bada Kula na gaggawa na MSF Bienfait Tombola ya ce tun bayan bullowar cutar suke samun mutane dake da dama dake zuwa asibitocin su inda wasu ma tafiyan su da nisa.

‎”Hada hannun da ma’aikatar lafiya, MSF da sauran jami’an lafiya suka yi ya taimaka wajen samar da kula wa masu fama da cutar cikin gaggawa sai dai yawan mutane dake ci gaba da kamuwa da cutar na nuna cewa ya kamata a kara zage damtse wajen samar da kula wa mutane da daukan matakan dakile yaduwar cutar.

Advertisement

Yin Allurar Rigakafi Da Samar Da Ruwa Mai Tsafta

‎Baya ga bai wa masu fama da cutar magani MSF na horar da jami’an lafiya, bude wuraren bai wa masu fama da cutar magani musamman a kauyukan da cutar ta bullo, wayar da kan mutane game da cutar, inganta gudanar da bincike domin gano yaduwar cutar, karfafa aikawa da mutanen manyan asibitoci domin samun kulan da ya kamace su da wayar da kan mutane matakan tsaftace ruwan Sha da tsaftace muhalli.

Advertisement

‎Kungiyar ta yi gargadin cewa duk da kokarin da suke yi yanayin yaduwar cutar ya fi matakan yakan cutar yawa.

‎MSF ta ce barkewar cutar Kwalara da sauran cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin amfani da ruwa mara tsafta ya fi faruwa a kauyukan dake fama da matsalolin rashin tsaftace ruwa da muhalli, rashin samun ingantattun asibitoci da dai sauran su.

Advertisement

‎Kungiyar ta ce yi wa mutane allurar rigakafin cutar da ma’aikatar lafiya ke shiryawa ba da mahimmanci wajen dakatar yaduwar cutar amma rigakafin zai dore idan an mai da hankali wajen wayar da kan mutane mahimmancin tsaftace ce ruwa, abinci da muhallinsu.

‎MSF ta ce za ta ci gaba da hada hannu da gwamnatin jihar Borno da ma’aikatar lafiya jihar domin ganin sun yaki cutar.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending