Connect with us

News

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 4 A Kaduna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

 

’Yan bindiga sun kashe mutum hudu ciki har da wani sabon malamin makaranta da aka dauka aiki a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.

Advertisement

 

Aminiya ta samu cewa lamarin ya faru ne a wasu kauyuka biyu – Gefe da Tudun Mare – na Karamar Hukumar.

 

Kakar Darakta Falalu Dorayi Ta Rasu

Harin da aka kai a Gefe ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku ciki har da shugaban matasan kauyen a daren ranar Lahadi.

 

Bayanai sun ce harin na biyu ya faru ne a Tudun Mare da ke Maraban Kajuru, inda aka kashe malamin makarantar mai suna Elisha Arziki.

Advertisement

 

Wani mazaunin yankin mai suna Bilyaminu ya ce an birne shugaban matasan da mutanen kauyen biyu a ranar Litinin.

 

“’Yan bindigar sun kashe shugaban matasan kauyen da wasu mutum biyu a lokacin da suka kai farmaki kauyen ranar Lahadi.

 

“An yi jana’izarsu a ranar Litinin yayin da kuma ‘yan bindigar suka kashe wani malami a kauyen Tudun Mare a daren ranar Litinin,” in ji shi.

Advertisement

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi alkawarin yin karin haske da zarar ya samu cikakken bayani.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending