News
Mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya faru a hanyar Legas zuwa Ibadan.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutane uku ne suka rasa rayukansu yayin da daya ya samu rauni a wani hatsarin da ya faru a hanyar Legas zuwa Ibadan, a yau Juma’a.
Hadarin dai ya hada da wata mota kirar Toyota Sienna mai lamba BDG 426 HT da wata mota kirar DAF mai lamba RNG 558 XC.
Daily trust ta rawaito cewa direban Sienna ya kutsa cikin motar DAF da ke fitowa daga wurin tirela.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta.
Okpe ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a kusa da gidan mai na Total dake kan babbar hanyar.
A cewarta, mutane bakwai ne suka hada da manya maza hudu, manya mata biyu da yaro daya.
Okpe ya alakanta musabbabin hadarin da gudu daga bangaren direban Sienna.
“An kai wanda aka jikkata zuwa babban asibitin Isaara domin kula da lafiyarsa yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na FOS, Ipara.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
