Connect with us

News

Ana Fuskantar Barazanar Karancin Man Fetur Da Tashin Farashinsa A Najeriya 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Dillalan Mai sunyi korafin cewar an samu karuwar farashin man fetur da suke sayowa daga Rumbunan ajiyar mai zuwa naira 720 akan kowacce lita daya, A yayin da mafi akasarin rumbunan ajiyar man suka kasance a kulle sakamakon karancin man da ake fuskanta, biyo bayan matsalolin da suka danganci canjin kudaden kasashen waje.

Sun baiyana cewar a saboda haka ana cigaba da rufe gidajen mai da dama a kowacce rana, wanda hakan kuma zai iya haifar da matsalar karancin man fetir a yan watanni masu zuwa a fadin kasar nan.

 

Da yake tabbatar da korafin dillalan man, Shugaban kanfanin mai na PETROCAM Trading Nig Ltd. Patrick Ilo, Ya ce man da kanfaninsa ya sayo har tan dubu 52 a Talatar data gabata, ya saye shi ne akan naira 720 kan kowacce Lita daya, batare da biyan wani tallafin mai a cikinsa ba.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Tace Watan Gobe Za’a Fara Rabawa Talakawa Naira Dubu 25

Y ace a sakamakon tashin farashin man da aka samu a halin yanzu, farashinsa zai iya kaiwa naira 729 akan kowacce Lita daya jahar Legas, idan har da gaske gwamnatin tarayya ta dena biya tallafin mai.

Ya dora alhakin tashin farashin man, da kalubale na canjin kudi, inda ya jaddada cewar har yanzu gwamnatin tarayya tana biyan tallafin mai ta bayan fage

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Tace Watan Gobe Za’a Fara Rabawa Talakawa Naira Dubu 25

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

 

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

 

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

 

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending