News
Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu litattafai a Daukacin Makarantu Masu Zaman Kansu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu litattafai a Daukacin Makarantu Masu Zaman Kansu dana Sakai a Fa’din Jihar.
Hakan ya biyo bayan tunasarwa da Bangarori daban daban sukai kan wasu illoli da suke cikin Litattafan da ake ganin sunci karo da koyarwar Islama.
Olusegun Obasanjo Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masana’antu
Hukumar Kulada Makarantu Masu Zaman Kansu ta fitar da Sanarwar Mai Dauke dasa hannun Hamisu Muhammad, Daraktan Tsare-Tsare da Bincike a Madadin Mataimakin Gwamna kan Makarantu Masu Zaman Kansu Baba Abubakar Umar.
Litattafan sune kamar haka:
*The Queen Primer (all editions) A Royal Series Published by Nelson Publishers Limited
*Basic Science for Junior Secondary School, Razat Publishers, 2018 edition. (for JSS3).
*Active Basic Science, 2014 edition By Tola Anjorin, Okechukwu Okolo, Philias Yara, Bamidele Mutiu, Fatima Koki, Lydia Gbagu.
*Basic Science & Technology for Junior Secondary Schools 1, 2 and 3: By W.K Hamzat, S. Bakare.
*New Concept English for Senior Secondary Schools for SSS2, Revised edition (2018 edition) by J Eyisi, A Adekunle, T Adepolu, F Ademola Adeoye, Q Adams and, J Eto.
*Basic Social Studies for Primary Schools by BJ Obebe, DM Mohammed, S N Nwosu, J A Adeyanju and ah Carbin
Bugu da Kari Shugaban Hukumar Tace Fina Finai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba AlMustapha sunyi Nasarar kama tarin Littafin Queen Primer da Gwamnatin ta haramta koyar dashi a Fa’din Kasar Kano.
A wani labarin kuma Olusegun Obasanjo Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masana’antu
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
