News
Hukuncin Kotun Koli: An Dawo Wa Da Al’ummar Kano Hakkinsu – Dr. Labaran
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana nasarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun koli a Ranar jumma, a matsayin dawo wa da jama’ar jihar Kano hakkinsu.
Dakta Labaran yana magana ne jim kadan bayan kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Yadda Harin Sojoji Ya Sauya Rayuwar Mutanen Tudun Biri A Jihar Kaduna
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa idan dai za a iya tunawa an gwabza kazamin fada tsakanin jam’iyyar adawa ta APC da kuma jam’iyyar NNPC mai mulki a fafutukar da ake yi na karbar kujera mafi daraja a jihar, inda a yau kotun koli ta mayar da ita ga jam’iyyar NNPP bayan ta sha kashi sau biyu a kotun sauraron kararrakin zabe da kotun daukaka kara a jere.
Dakta Labaran ya nuna farin cikinsa da cewa, wannan hali na rashin girgiza na mai girma Gwamna ya cancanci yabo, saboda kawai ci gaba ya yi da gudanar da shugabanci nagari ta hanyar shimfida ayyukan da jama’a ke bukata ba tare da la’akari da munanan kalubalen da lamarin ya jawo jihar ba, ya kara da cewa hakan ya nuna gwamna yana da zuciya mai karfi tare da mayar da lamuransa ga Allah.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa wannan nasara ta al’ummar jihar Kano ce da aka kusa kwace wa hakkinsu, haka kuma nasara ce ta Nijeriya da dimokuradiyya saboda an tabbatar da hukuncin da ‘yan kasa suka yanke, wanda shi ne manufa ta tsarin mulkin dimokuradiyya a duk fadin duniya.
“A madadin kaina, da iyalaina, da ma’aikatar lafiya, da dukkan hukumominta, ina mika sakon taya murna ga Alhaji Abba Kabir Yusuf, ‘yan majalisar zartarwa na jiha da shugabannin babbar jam’iyyarmu ta NNPP da al’ummar jihar Kano, da ‘yan Kwankwasiyya masu rajin kawo sauyi a ko ina suke a duniya kan wannan nasara mai cike da tarihi.
“Haka kuma ina mika irin wannan ga Jagoran tafiyar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa samun wanna nasara. Yallabai, kwarewarka a siyasa da hidimta wa jama’a da ka yi su suka kara daraja ka har ka zama mai nasara a dimokuradiyya, ka tsallake dukkan wani tarnaki na siyasa da aka jefo maka”, ya bayyana cikin farin ciki.
Dakta Labaran ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a ci gaba da sauye-sauyen tsarin kiwon lafiya da mai girma gwamna ya fara ta yadda za a samu dauwamammen ci gaba mai dorewa, da sauran dukkan bangarorin rayuwa don inganta rayuwar al’ummar jihar kamar yadda yake kunshe cikin kundin gudanar da mulkinsa, yana mai gode musu bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnati bisa kyakkyawan salon mulkinta.
A karshe ya yaba wa alkalan da suka tabbatar wa al’umma hakkinsu, inda ya bukaci magoya baya da su yi bukukuwa cikin lumana tare da gode wa Allah Madaukakin Sarki.
