News
Tashin farashin kayan abinci ya tilasta yawancin magidanta kasa ɗora tukunya sau uku a rana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tashin farashin kayan abinci ya yi ƙololuwar da ta kai shi har kashi 28.92 cikin 2023. Wannan lamari ya haddasa tsadar rayuwar da ta galabaita miliyoyin ‘yan Najeriya a ahekarar, har ta kai gidaje da dama ba a iya ɗora girki sau uku a rana kamar yadda ɗan Adam ya ke yi a rayuwar sa.
Cikin watan Nuwamban 2023 tsadar ta kai kashi 28.20, amma zuwa Disamba sai da malejin ya dangwale har kashi 28.92.
Wannan ƙididdiga dai ta fito daga Ofishin Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai na Ƙasa (NBS), wanda mallakar Gwamnatin Tarayya ne.
Ƙididdigar wadda aka fitar ranar Litinin, ta nuna cewa tsadar kayan abinci ta ƙaru da 0.72 tsakanin Nuwamba zuwa Disamba 2023.
NBS ta ce amma idan aka auna tsadar rayuwar 2022 da ta 2023, to za a ga cewa a Disamba 2022 malejin ya na kashi 21.34 ne, amma kuma a Disamba 2023, ya dangwale kashi 28.92.
Farashin abinci ya dangana 33.93 a Disamba 2023 idan aka kwatanta da farashin Disamba 2022 lokacin da ya ke kashi 23.75.
Watannin tsakiyar 2023 ne kayan masarufi da na sauran nau’ukan kayan da ake sarrafawa cikin gida suka yi tashin-gwauron-zabo, saboda cire tallafin fetur da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Premium Times ta ruwaito cewa Lamarin ya sa tsadar fetur ta buwayi kowace sana’a ko aiki a faɗin ƙasar nan. Bincike ya nuna cewa gidaje da dama ana fashin daga abinci sau uku a rana. Wasu kuma ana fashin dafawar ma ɗungurugum a wata ranar.
A wani labarin kuma Dalilin ci gaba da garkuwa da mutane, duk da an yi wa layukan waya rajista da lambar katin ɗan ƙasa, NIN – Pantami
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
