News
Yanayin Tsadar Rayuwa A Najeriya Ya Yi Tashin Roket Fiye Da Tunanin Mai Tunani.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen bukukuwa da shagulgulan Babbar Sallah, malejin tsadar rayuwa a Najeriya ya yi tashin roket fiye da tunanin mai tunani.
Hakan na faruwa ne daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayya ke ta gugumarar kasa tsayar da ƙayyadajjen mafi ƙanƙantar albashi ga ma’aikatan ƙasar nan, waɗanda har yau akwai jihohin da ba su iya biyan Naira 30,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi.
Yayin da aka shekara dindi har da ɗoriya ana fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, tun bayan cire tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi, malejin tsadar rayuwa ya ƙaru sosai daidai gabatowar Babbar Sallah.
Premium Times ta ruwaito cewa Ragunan layya sun yi tsadar da ba su taɓa yi ba a tarihi, inda a garuruwa da dama har ana samun ragon da ya haura Naira miliyan 1.
Haka nan kayan miya kusan a ce sun gagari talaka tun ma kafin ruwan shuka, ta yadda gidajen marasa galihu da dama sun daina haɗa cefanen kayan miya, sai dai a kaɗa kuka kaɗai.
Jama’a da dama na ci gaba da bayyana tsananin damuwar su dangane da tsadar kayan abinci da kayan miya daidai lokacin shirye-shiryen Sallah.
Wake tiya ɗaya tadda ke Naira 1,800 kusa da azumi, yanzu ta dangwale Naira 5,000, ko saye ko bari.
A shafukan sada zumunta na Facebook kuwa, wasu da dama na tura hoton kayan miyar da suka sayo domin abincin Sallah, tare da bayyana kuɗin da suka sayi kayan miyar.
Wani da ya sayo kayan miyar Naira dubu 40 a Jihar Sokoto, ya ɗauki hankalin jama’a da dama.
A ɗaya ɓangaren kuma, Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta yi tilawar malejin tsadar rayuwa a watan Mayu, inda ta ce ya yi tashin roket zuwa kashi 33.95, daga 33.69 a watan Afrilu.
Haka dai NBS wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya ta bayyana, a ranar Asabar, jajibirin Babbar Sallah.
NBS ta ce idan aka kwatanta da watan Mayu na shekarar 2023, an samu ƙarin hauhawar tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci da kayan masarufi da kashi 11.54 a cikin shekara ɗaya, wato zuwa watan Mayu, 2024.
Ofishin NBS ya ce malejin tsadar rayuwa ya na kashi 22.41 a watan Mayu, 2023, yayin da yake 33.96 yanzu a watan Mayu, 2024.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion7 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
