News
Kotun Koli Ta Sanar Da Ranar Da Alkalin Alkalan Najeriya Zai Yi Ritaya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun koli ta sanar da cewa Olukayode Ariwoola zai yi ritaya a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya a ranar 22 ga watan Agusta.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Festus Akande mai magana da yawun kotun koli ya ce za a gudanar da zaman kotun na ban kwana domin girmamawa ga alkalin alkalan wanda ke cika shekaru 70 na ritaya.
Zanga-zanga: Gwamnati ta fara sayar da buhun shinkafa N40,000
Akande ya kuma ce kotun kolin ta fara hutun ta na shekara a ranar 22 ga watan Yuli inda za ta dawo a ranar 23 ga watan Satumba na 2024 kamar yanda Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito
“Shekarar aiki ta 2023/2024 ta zo karshe a ranar Juma’a 19 ga watan Yuli na 2024″, inji sanarwar.
” Kotu ta fara hutu a ranar Litinin 22 ga watan Yuli na 2024 kuma za ta dawo a ranar 23 ga watan Satumba na 2024.”
A ranar 12 ga watan Oktoba na 2022 ne dai tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin alkalin alkalan Najeriya wata 4 bayan ajiye aikin da Ibrahim Muhammad ya yi.
