News
Hukumar Hisbah Ta Ceto Ƙananan Yara Mata 16 Daga Hannun Masu Fataucin Mutane A Kano.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jami’an Hisbah na Jihar Kano aikin da suka gudanar kwanan nan ya kai ga ceton ƙananan yara mata 16 da ake fataucin su zuwa ƙasashen waje.
An kama yaran ne a tashar mota ta Unguwa Uku a Kano, inda aka same su suna shiga cikin wata mota da za ta tafi Lagos.
Karin Kashi 50% Na Farashin Data Da Na Kiran Waya Zai Kayo Cikas Ga Tsarin Koyo Da Koyarwa —Dalibai
A cewar Mataimakin Kwamandan Hisbah, Mujahid Aminuddeen , yaran zasu nufi ƙasar Benin da Ghana, inda za a yi amfani da su. “Jami’anmu a tashar motar sun kama waɗannan yara ƙanana, ,” in ji Aminuddeen.
Aminuddeen ya yi kira ga iyaye su kula sosai da lafiyar ‘ya’yansu fiye da neman abin duniya. “Abin mamaki ne yadda wasu mutane ke son biyan kuɗaɗe masu yawa don a fatauci su, duk da haɗarin fyade, cin zarafi, har ma da mutuwa,” in ji shi.
-
News15 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
