Connect with us

News

Fursunoni 53,254 Ke Jiran Shari’a A Najeriya – Rahoto

Published

on

Fursunoni 53,254 ke jiran shari’a Najeriya

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rahotanni daga Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) sun bayyana cewa akalla fursunoni 53,254 ne ke jiran shari’a a gidajen yari daban-daban a fadin kasar nan.

Advertisement

Wannan adadi na karshe da aka sabunta a ranar 24 ga Fabrairu, 2025, ya nuna cewa yawan fursunonin da ke a gidajen yari ya kai 80,100, inda kawai 26,846 daga cikinsu ne aka yanke wa hukunci.

Me ya sa sojojin Najeriya ke yawan kai hari kan fararen hula ‘bisa kuskure’?

Yawaitar fursunonin da ke jiran shari’a na kara jaddada matsalar jinkiri a tsarin shari’a na Najeriya, wanda ke haddasa cunkoson da ake fuskanta a gidajen gyaran hali.

Advertisement

A watan Janairu 2025, Shugaban Riko na Hukumar NCoS, Sylvester Nwakuche, ya sha alwashin daukar matakan rage yawan fursunonin da ke jiran shari’a da kuma inganta harkokin kulawa da gidajen gyaran hali.

Haka nan, Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa daga nan zuwa ranar 1 ga Oktoba, 2025, za a fito da cikakken tsari na gyaran fuska da zai sauya yanayin gudanarwa a gidajen gyaran hali.

Advertisement

Ministan ya ce:“Bai dace kawai a rika tantance fursunoni ba ba tare da daukar matakan da suka dace wajen sauya tsarin kula da gidajen gyaran hali ba. Muna kan aiwatar da matakin farko, sannan mataki na biyu yana gudana. Nan da Oktoba, za mu fito da cikakken rahoto kan matakan da za a dauka don sauya fasalin gidajen gyaran hali a Najeriya.”

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending