News
Amb. (Dr) Maimuna Umar Sheriff Za Ta Isar da Rahoton Gobarar Fagge Ga Gwamnan Kano Domin Neman Daukin Gaggawa
Amb. (Dr) Maimuna Umar Sheriff, mai ba wa Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin Community Policing, ta bayyana cewa za ta isar da rahoton gobarar da ta shafi Babban Ofishin ‘Yan Sanda na Fagge ga Gwamnan domin neman daukin gaggawa.
Gobarar, wadda ta tashi a Babban Ofishin ‘Yan Sanda da ke unguwar Fagge, ta haddasa asarar muhimman kayayyaki da dama, ciki har da babura, takardu masu muhimmanci, da kuma lalacewar wasu kayayyakin aiki na jami’an tsaro.
Amb. Maimuna ta bayyana cewa, duk da gaggawar da ake bukata wajen farfado da ayyukan ofishin. hakan zai samar da ci gaba da walwala ga al’ummar yankin tare da kuma tabbatar da lafiyar al’umma da kare dukiyoyinsu.
“Fagge cibiyar kasuwanci ce mai matukar muhimmanci, don haka samar da tsaro mai inganci a yankin zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da inganta harkokin kasuwanci,” in ji ta.
Amb. Maimuna ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin zamanantar da ofishin ta hanyar sanya kwamfutoci da kayan aikin zamani domin bunkasa ayyuka da kuma inganta adana bayanai yadda ya kamata.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
