News
Zanga-Zangar Dalibai Ta Tilasta Rufe Kwalejin Adamawa Na Tsawon Mako Daya
Hukumar Kwalejin Fasaha ta Jihar Adamawa (Adamawa State Polytechnic, Yola) ta sanar da rufe makarantar na tsawon mako guda, bayan wata zanga-zangar dalibai da ta ɓarke sakamakon matsalolin rashin ruwa da lantarki.
Daliban makarantar sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin, suna bayyana fushinsu kan matsanancin rashin wadatar ruwa da hasken lantarki da suke fuskanta a harabar makarantar. Wannan ya tilasta hukumar makarantar ɗaukar matakin dakatar da karatu na wucin gadi, domin bai wa hukumomi damar shawo kan matsalolin.
MARTANI: Jama’ar Goronyo Sun Kare Minista Bello Goronyo Daga Zargin Mu’azu S. Rima
A wata sanarwa da rajistaran makarantar, Simnawa Ayuba, ya fitar, an bayyana cewa an rufe makarantar ne domin ba da damar gyaran lantarki cikin gaggawa. “An ɗauki matakin rufe makarantar domin bai wa hukumomi damar gyara tsarin lantarki,” in ji sanarwar.
Hukumar makarantar ta umarci dukkan dalibai da su fice daga harabar kwalejin kafin ƙarfe 12:00 na rana a yau Litinin, tare da jan hankalinsu da su kasance masu bin doka da oda.
Har yanzu, ba a bayyana takamaiman ranar da za a sake buɗe makarantar ba, sai dai sanarwar ta ce ana sa ran dawo da karatu bayan mako guda idan an kammala gyare-gyare.
