Connect with us

Politics

Ba Za Mu Bawa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugabancin Kasa A Jam’iyyarmu Ba  —NNPP

Published

on

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana a hukumance cewa ba za ta sake ba wa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, damar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar a babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Agbo Major, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 5 ga watan Yuli, 2025.

Advertisement

Yadda Cutar Amai da Gudawa Ta Kama  Dalibai 81 A Makarantar Gwamnati A Kaduna

Sanarwar ta zo ne a matsayin martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya bayyana a kwanakin baya cewa Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa cikin NNPP kuma zai tsaya takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar.

Galadima ya ƙara da cewa babu wata alamar da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa jam’iyyar APC, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, inda ya jaddada cewa “muna nan a NNPP kuma muna tare da Kwankwaso har 2027.”

Advertisement

Sai dai a cewar Dr. Agbo Major, “Kwankwaso da Galadima tuni an kore su daga jam’iyyar NNPP bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da sabawa dokokinta.”

Ya ce, “Kwankwaso ba zai iya amfani da jam’iyyar NNPP don cimma wata manufa ta siyasa ba, domin kuwa tun bayan zaɓen 2023, jam’iyyar ta yanke duk wata alaƙa da Kwankwasiyya Movement.”

Advertisement

A cewarsa, jam’iyyar na ci gaba da ɗaukar matakan sake farfaɗo da martabarta da kuma tabbatar da daidaito a cikin gida, domin fuskantar babban zaɓen 2027 ba tare da rabuwar kai ba.

Jam’iyyar NNPP dai na daga cikin. jam’iyyun da suka fi ɗaukar hankalin jama’a a zaɓen 2023, musamman a jihar Kano, inda ta samu rinjaye mai faɗi. Sai dai rikicin cikin gida da ya biyo baya ya haifar da rabuwar kawuna tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, wanda ya kai ga kore Kwankwaso da wasu daga cikin masu biyayya gare shi.

Advertisement

NNPP ta jaddada kudirinta na gudanar da cikakkiyar tsari mai ma’ana domin fuskantar kalubalen zaɓen 2027 cikin haɗin kai da saukin kai.

 

Advertisement

KAKAKI24

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending