Connect with us

Sports

Liverpool ta yi yarjejeniya da Bellingham, Ajax ta gaya wa Man Utd matsayarta kan Antony

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

Advertisement

 

Liverpool ta kulla yarjejeniya ta baka da dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund, Jude Bellingham inda matashin dan wasan na Ingila mai shekara 19 zai koma Anfield a watan Janairu. (Football Insider)

Advertisement

Ajax ta bukaci Manchester United ta biya sama da Fam miliyan 84, idan tana son daukar dan wasan Brazil, Antony. (Mail)

Sannan kuma Ajax din ta tuntubi Aston Villa a kokarin da take yi na sayen Anwar El Ghazi, mai shekara 27, domin maye gurbin Antony, idan ya koma Old Trafford.

Advertisement

Sai dai ita ma PSV Eindhoven na sha’awar sayen dan wasan Aston Villa dan kasar Holland. (Mirror)

Dan bayan Tottenham Sergio Reguilon, na dab da kulla yarjejeniyar tafiya Atletico Madrid, domin buga wasannin aro, inda kungiyar ta Sifaniya take neman wanda zai maye gurbin Renan Lodi, dan Brazil, wanda zai koma Nottingham Forest. (Times – subscription required)

Advertisement

Golan Slovakia Martin Dubravka, mai shekara 33, ya gaya wa Newcastle cewa yana son barin kungiyar domin tafiya Manchester United. (Sky Sports)

Liverpool na sa ido kan dan wasan tsakiya na Wolves, Ruben Neves, dan Portugal mai shekara 25, da kuma dan wasan tsakiya na RB Leipzig, Konrad Laimer, dan Austria mai shekara 25. (90min)

Advertisement

Aston Villa ta cimma yarjejeniyar sayen dan bayan Southampton da Poland Jan Bednarek, mai shekara 26. (Football Insider)

Haka kuma Villa din na son neman kudin da za ta dauki dan bayan West Ham, Craig Dawson inda za ta ba dan Ingilar kwantiragin shekara biyu. (Sun)

Advertisement

Chelsea na shawarar ko ta soke kwantiraginta da dan wasan tsakiya na Ingila Ross Barkley wanda a yanzu take biyansa kusan Fam dubu 200 a duk mako. (Sun)

West Ham are na tattaunawa da tsohon dan wasan gaba na gefe na Manchester United, Adnan Januzaj domin dawo da shi gasar Premier, wanda bai da kwantiragi tun bayan da ya bar Real Sociedad. (Talksport)

Advertisement

Haka kuma Hammers din na shirin sake taya dan wasan tsakiya na Club Bruges da Belgium, Hans Vanaken, mai shekara 30, a karo na uku. (Mail)

Edinson Cavani, wanda ya kasance ba shi da kungiya bayan da ya bar Manchester United, na son tafiya gasar La Liga a bazaran nan, inda Valencia da Real Sociedad ke sha’awar dan wasan na Uruguay mai shekara 35. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Wolves ta dage wajen tattaunawa da Stuttgart, domin sayen dan gaban Austria Sasa Kalajdzic kan Fam miliyan 17. (Mail)

Brighton na sha’awar sayen matashin dan bayan Rosario Facundo Buonanotte dan tawagar Argentina kuma a shirye take ta biya abin da ya haura Fam miliyan uku a kansa. (Athletic – subscription required)

Advertisement

Bournemouth na neman yi wa Leeds United shigar sauri ta saye matashin dan wasan gaba na Zurich dan Italiya Willy Gnonto, mai shekara 18. (Football Insider).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending