News
Gobara ta hallaka sojoji 15
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gobara a sansanin sojin Armenia ta yi sanadiyyar rasuwar sojoji 15 sannan uku kuma na cikin mawuyacin hali.
Gobarar ta barke ne da sanyin safiyar Alhamis a wani sansani kusa da iyakar ƙasar da Azerbaijan.
Rahotanni sun ce wutar ta tashi ne sakamakon rashin bin ka’idoji.
Sai dai Firaminista Nikol Pashinyan, ya bayyana cewa sojojin na amfani da man fetur wajen kunna na’urar yin girki.
Advertisements
