Connect with us

News

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Sojin jumhuriyar Nijar Ta Yanke Hulda Da Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Gwamnatin sojin Nijar ta katse huldar diflomasiyya da Najeriya, Togo, Amurka da kuma ta fuskar tsaro da tsohuwar uwargijiyar kasarsu Faransa.

Gwamnatin sojin Nijar din ta kuma ki ganawa da wakilan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura domin tattaunawa da ita.

Advertisement

Jam’iyyar PDP ta caccaki jam’iyyar APC akan zaben Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Wani daga cikin wakilan ya shada da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kasa da awa 24 da isarsu birnin Yamai suka baro kasar Nijar, “ko kwana ba mu yi ba,” ballantana ganawa da Janar Abdourahamane Tiani kamar yadda aka tsara.
A ranar Laraba ne ECOWAS ta tura wakilan nata, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulki sojin Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, domin tattaunawa da gwamnatin sojin da ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.

Da farko dai gwamnatin Najeriya ta sanar cewa kwamitin na Abdulsalami Abubakar zai gana da Janar Tiani inda zai gabatar wa gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Nijar bukatun ECOWAS.

Advertisement

Kungiyar wadda Shugaan Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta, ta kakaba wa gwamnatin sojin ta Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sannan a ranar Lahadi ta ba wa sojojin wa’adin mako guda su mika wa Bazoum mulkinsa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending