Politics
Jam’iyyar APC ta lashi takobin kama duk wani dan Najeriya mazauna amurka da ya yi zanga-zangar adawa akan Tinubu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu yan Najeriya sun bayyana damuwarsu ga Jaridar Sahara Reporters cewa ana kokarin hanasu bayyana damuwarsu ta hanyar zanga-zanga wa shugaban kasar Najeriya a wani taro da Shugaban kasa Tinubu zai gabatar a ranar 20 ga watan Satumba mai zuwa. A birnin New York na kasar Amurka.
Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban jam’iyyar APC reshen Amurka, Farfesa. Tai Balofin, ya yi ikirarin cewa wani dan jam’iyyar da aka dakatar, Adesegun Labanjo ne ya shirya taron.
Wasu ma’aikatan Babban Bankin Kasa CBN na amsar Albashi fiye da ministoci – RMAFC
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “A kwanan nan ya zo mana cewa wasu mutane na shirin gudanar da wani gangami a ziyarar da shugaba Tinubu ya kai Majalisar Dinkin Duniya. Wannan gangamin da aka shirya kai tsaye ya mayar da martani ne ga taron da wani dakataccen Malam Labinjo ya shirya wanda ke ikirarin shi ne Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, a ranar 20 ga Satumba, 2023.
Wani labarin kuma Wasu ma’aikatan Babban Bankin Kasa CBN na amsar Albashi fiye da ministoci – RMAFC
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro