News
NDLEA Ta Bankado Kungiyar Da Ke Amfani Da Mahajjata Wajen Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wasu shugabanni uku na wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi, wadda ke amfani da mahajjata a matsayin hanyar fitar da ƙwayoyi zuwa ƙasar Saudiyya.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce an cafke Abubakar Muhammad, Abdulhakeem Tijjani da Muhammad Aji Shugaba, bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri da suka kai ga kama wasu mahajjata biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano.
Farfesa Dahiru Sale: Za Mu Tabbatar Kano Ta Ci Gajiyar Shirin TVET
An kama mahajjatan biyu, Ibrahim Mustapha da Muhammad Shifado, a lokacin da suke shirin hawa jirgin Ethiopian Airlines ET 940 domin gudanar da aikin Hajji a birnin Jeddah.
Babafemi ya ce, “Binciken da muka gudanar da na’urar gano abin da ke cikin ciki ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargi sun haɗiye ƙwayoyi. Kowannensu ya fitar da kunshi 45, wanda ya kai adadin kunshi 90 da nauyin su ya kai 1.04kg na cocaine.”
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa waɗannan mahajjatan suna aiki ne karkashin wani tsarin mugunta da wasu ke jagoranta da nufin fitar da miyagun ƙwayoyi ta hanyar da ba za ta sa jami’an tsaro su zarga su ba.
Bayan samamen da jami’an hukumar suka gudanar a ranakun Talata da Laraba, 27 da 28 ga Mayu, an cafke jagororin ƙungiyar a Kano, inda yanzu haka ake ci gaba da zurfafa bincike domin gano sauran mambobi da kuma hanyar da suke amfani da ita wajen safarar ƙwayoyin.
NDLEA ta jaddada kudirinta na ci gaba da kai wa ga ƙungiyoyin da ke safarar miyagun ƙwayoyi, musamman wadanda ke amfani da hanyoyin ibada wajen aikata laifi.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News5 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
