News
Yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni daga Jihar Imo na cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC na gundumar Umuchoke a garin Okwe da ke cikin karamar hukumar Onuimo.
Mutumin mai suna Christian Ihim ya rasa ransa ne yayin da ‘yan bindigan suka kai wani hari zuwa gidansa ranar Talata da dare.
NUJ ta kori Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA daga Kungiyar.
Baya ga halaka shi, ‘yan bindigan sun kuma sace wasu jami’an jam’iyyar ta APC biyar.
Daga nan rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun isa kauyen Okwelle inda suka sace wata jami’ar APCn mai suna Onyinyechi Egenti.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar ta Imo, Henry Okoye ya tabbatar da aukuwar hare-haren amma ya bukaci a ba shi karin lokaci domin tattaro cikakken bayani kan batun.
Shi ma kakakin jam’iyyar ta APC a Imo, Cajethan Duke ya sanar da manema labarai kisan Mista Ihim, da kuma sace jami’ansu na APC.
