News
Ambaliyar ruwa tayi Sanadiyar mutuwar mutum uku a Jahar Kebbi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama a nayi a ranar Asabar a unguwar Dakingari da ke karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, an tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon ruwan sama.
Shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Muhammad Lawal Suru, ya tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon ambaliyar ta haka kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.
Ya ce bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ke gangarowa daga tsaunukan da ke kewayen garin Dakingari ya taimaka wajen ambaliyar a yankin .
Ya ce, “Sama da shekaru ashirin suna fama da ambaliyar ruwa lokacin da ake ruwan sama.
Gwamnatocin baya na Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar amma hakan bai hana faruwar ambaliyar ruwa a duk shekara ba.”
A cewarsa, za a iya hana ambaliyar ruwa idan za a iya gina shingen mashigar ruwa a kewayen tsaunukan.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su daina kafa gine-gine a magudanar ruwa, da kuma zubar da shara ba gaira ba dalili.
