Connect with us

News

Wasu Yara  3 Sun Mutu Sanadiyyar Ci Abinci Mai Guba A Katsina

Published

on

Abinci

Wasu yara uku sun rasu yayin da wata ta tsira bayan sun ci abinci da ake zargin yana ɗauke da guba a unguwar Magama da ke karamar hukumar Jibia a Jihar Katsina.

Yaran da suka mutu su ne Hussaina Ayuba, Ahmed Ayuba da Nana Ayuba, kamar yadda wani masani a harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana a ranar Alhamis.

Advertisement

‎MATSALAR TSARO A NAJERIYA: Akalla Mutune 590 Ne Suka Rasa Rayukansu Yayin Da Aka Sace 192 A Watan Afrilu  ‎ ‎– Rahoto

Rahotanni sun nuna cewa yaran sun ci taliya ce da ake zargin an zuba mata guba, lamarin da ya kai su asibitin gwamnati na Jibia inda aka tabbatar da mutuwarsu.

Sai dai wata yarinya mai suna Hafsat Ayuba, mai shekara 12, ta tsira daga gubar, kuma tana ci gaba da samun sauƙi karkashin kulawar likitoci.

Advertisement

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wata mata mai suna Fatima Abdulƙadir, mai shekara 20, wadda ake zargin ita ce ta dafa abincin. Haka kuma, an cafke wasu mutum biyu da ake kyautata zaton suna da hannu a lamarin.

’Yan sanda sun ce sun kai bincike wajen da abin ya faru, kuma ana ci gaba da zurfafa bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma wadanda ke da hannu a ciki.

Advertisement

An riga an yi jana’izar waɗanda suka mutu bisa tsarin addinin Musulunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending