Connect with us

News

Jam’iyyar PDP Ta Musanta Tsayar da Ɗan Takarar Gwamna a Nasarawa

Published

on

IMG 20250716 WA0002

DAGA ZUBAIRU LAWAL, LAFIA

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Nasarawa ta musanta jita-jitar cewa ta tsayar da wani mutum guda a matsayin ɗan takararta na gwamna a zaben shekarar 2027, tana mai bayyana hakan a matsayin matakin da bai samu amincewar jam’iyyar gaba ɗaya ba.

Advertisement

Shugabannin jam’iyyar daga ƙananan hukumomi 13 na faɗin jihar ne suka bayyana matsayinsu a wata ganawa da manema labarai da suka gudanar a zauren ’yan jarida na Lafia, babban birnin jihar, a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025.

Shugaban Amurka Trump Ya Yi Barazanar Kakaba Wa Kasashen Afirka Haraji

Shugaban ƙungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar, Comrade Jibrin Idris Ibrahim, ne ya jagoranci taron. Ya ce:

Advertisement

“PDP jam’iyya ce da ke kan tafarkin dimokuraɗiyya, ba mallakin mutum ko ƙungiya ba ce. A halin yanzu, babu wani ɗan takarar da jam’iyyar ta amince da shi a hukumance domin zaben 2027.”

Comrade Jibrin ya bayyana cewa taron da wasu mutane suka gudanar a ranar 10 ga Yuli, 2025, a gidan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Mr. Francis Orogu, don tsayar da wani ɗan takara, bai da inganci, kuma ba ya wakiltar matsayin jam’iyyar a matakin jiha.

Advertisement

Ya kuma bayyana damuwa kan yadda wasu ke kokarin karkatar da tsarin jam’iyya ta hanyar yanke hukunci ba tare da izini ko cikakken sahalewar bangarorin jam’iyya ba.

“PDP ta buɗe ƙofa ga duk wanda ke da sha’awar takara. Ba za mu amince da tsarin da ke tauye damokuraɗiyyar jam’iyyar ba. Dole a bi ka’ida da doka.”

Advertisement

A kan haka, Comrade Jibrin ya bukaci kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar da ya ɗauki matakin ladabtarwa kan Mr. Orogu da sakataren jam’iyyar na yankin tsakiya da dukkan waɗanda ke da hannu wajen tallata wani ɗan takara ba bisa ƙa’ida ba.

A ƙarshe, ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su zauna lafiya da juna, su girmama juna, tare da ci gaba da tattaunawa da manyan jiga-jigan jam’iyya don fuskantar babban zaben 2027 da kwarin gwiwa da ɗaukaka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending