Connect with us

News

DSS Ta Cafke Matashi Da Ke Safarar Bindigogin AK-47 Da Bom-Bom Na RPG A Kano

Published

on

Arms Courier (1)

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Abubakar Muhammad, bisa zargin safarar makamai masu haɗari zuwa garin Funtua da ke Jihar Katsina.

Jami’an DSS sun kama wanda ake zargin ne a Ƙaramar Hukumar Gezawa bayan samun bayanan sirri da suka kai ga tare shi yayin da yake ƙoƙarin jigilar makaman zuwa inda aka tura shi.

Advertisement

Fassarar Jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Na Ranar Dimokradiyya

Makaman da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da bindigogin AK-47 guda uku, bom-bom na makamin roka (RPG) guda huɗu da kuma kwanson harsasai guda biyu.

Advertisement

Majiyoyi sun ce binciken farko ya nuna cewa an ɗora wa Abubakar aikin jigilar makaman ne daga yankin Maigatari da ke Jihar Jigawa zuwa Funtua, inda aka yi masa alkawarin biyan Naira 450,000 bayan ya kai kayan ga wanda ake sa ran zai karɓe su.

Da yake amsa tambayoyin jami’an tsaro, wanda ake zargin ya amince da cewa shi ne ke jigilar makaman. Ya bayyana cewa da farko ya ƙi karɓar aikin, amma daga bisani ya amince bayan matsin lambar da aka ci gaba da yi masa.

Advertisement

Ya kuma yi ikirarin cewa bai taɓa shiga irin wannan aiki a baya ba, tare da nuna nadama kan lamarin.

A cewar DSS, kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna motsin wanda ake zargin a hanyar Kano zuwa yankin Funtua, wani yanki da ke fama da matsalolin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga.

Advertisement

Hukumar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen da ake zargin suna da alaƙa da safarar makaman.

DSS ta kuma tabbatar da cewa tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano tare da rusa hanyoyin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY NEWS 24

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending