Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Ten Hag, Rashford, Martial, Wan-Bissaka, Nkunku, Kamara, Guimaraes

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Manchester United za ta sayar da ‘yan wasanta irinsu Marcus Rashford ɗan Ingila, da mai buga gaba asalin Faransa Anthony Martial, da ɗan wasan baya asalin Ingila Aaron Wan-Bissaka, ɗan kasar Ivory Coast da ke buga tsakiya Eric Bailly, da tsohon mai tsaron baya Phil Jones da ɗan ƙasar Brazil da ke buga baya Alex Telles a wani gagarumin garambawul da take shirin aiwatarwa karkashin sabon kocinta Erik ten Hag a wannan kakar. (Sun)

Ɗan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice, mai shekara 25, na cikin jeren mutanen da Ten Hag ke fatan ɗaukowa. (Guardian)

Mai buga tsakiya a Netherlands Donny van de Beek, ya shirya komawa hannun tsohon kocinsa na Ajax a Old Trafford, idan kwantiraginsa ya kare a Everton. (Sun)

Advertisement

Sabbin ‘yan wasan tsakiya a baya, da masu buga tsakiya biyu da mai buga gefe da kuma kai hari su ne irin mutanen da Manchester United ke son sayowa, kuma za ta bai wa fifiko a bana. (Sky Sports)

Manchester United ta ƙi amincewa da bukatar Ten Hag na dawo da tsohon mataimakin Sir Alex Ferguson, Steve McClaren domin su yi aiki tare. (Telegraph)

RB Leipzig ta dage kan cewa ba za ta sayar da ɗan wasanta na tsakiya ba asalin Faransa, Christopher Nkunku, mai shekara 24, duk da zawarcinsa da ake yi a Manchester United da Arsenal. (Sky Sports Germany – in German)

AC Milan na iya mika tayi kan ɗan wasan Chelsea dan asalin Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 28. (Goal

Advertisement

Burnley na farautar kocin riƙo a Wales Rob Page, mai shekara 47, domin maye gurbin Sean Dyche. (90Min)

Everton ta bi sahun Tottenham a farautar ɗan wasan nan mai shekara 29 da ke taka leda a West Brom kuma mai tsaron raga a Ingila Sam Johnstone. (Mirror)

Real Madrid na sanya ido kan ɗan wasan Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 24. (AS – in Spanish)

Dan wasan Besiktas da Turkiyya Ridvan Yilmaz, mai shekara 20, ya ja hankalin Tottenham da wasu manyan ƙungiyoyi a Turai. (TRT Spor – in Turkish)

Advertisement

Kocin Aston Villa Steven Gerrard ya nuna zawarcinsa kan ɗan wasan Marseille Boubacar Kamara, mai shekaru 22, lokain da ya kalli wasan da kungiyar ta Faransa ta doke Nantes a ranar Laraba. (Daily Mail)

Villa ta matsu matuƙa ta kulla yarjejeniyar dindindin da ɗan wasan Roma asalin Sweden mai shekara 32 da ke tsare raga, Robin Olsen. (Football Insider)

Ɗan wasanParis St-Germain da Argentina Angel di Maria, mai shekaru 34, ya ja hankali Juventus da ke son saye shi idan kwantiraginsa ya kawo karshe. (Gianluca di Marzio)

Leicester City na kokarin doke Tottenham a cinikin ɗan wasan Brazil Gleison Bremer, ɗan shekara 25, da ke taka leda a kungiyar Torino ta Italiya.(Telegraph)

Advertisement

Calvin Ramsay na Aberdeen mai shekara 18, Liverpool ta kwadaitu da shi bayan bajinta da ya nuna a wasannin ‘yan kasa da shekaru 21 Scotland. (Liverpool Echo)

Mai buga tsakiya aSwansea Flynn Downes, ɗan shekara 23, ya ce bai damu da rade-radin da ake yaɗawa na alakatanshi da Leeds United. (Wales Online)

Manchester City da Newcastle na farautar ɗan wasa mai shekara 18 daga Rangers Alex Lowry, mai buga tsakiya. (Football Insider)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *