Politics
Jam’iyyar APC Ta Ce Zafin Shan Kaye Ne Ke Damun Atiku
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, da ya rungumin ‘kaddarar shank aye a zaben shugaban kasa da ya gabata.
A yayin wani taron manema labarai da Atikun ya shirya a jiya, Ya yi kira ga sauran ‘yan takarar shugaban kasa zaben da ya gabata dasu mara masa baya, domin yaki da amfani da takardun kammala karatu na bogi, da yake zargin shugaban kasa Bola Tinubu na amfani dasu.
Ana Fuskantar Barazanar Karancin Man Fetur Da Tashin Farashinsa A Najeriya
To sai dai a martanin da jam’iyyar APC ta mayar dangane da shirya taron manema labaran, ta hannun kakakinta, Felix Morka, Ta baiyana cewar taron manema labaran a matsayin na fanko wanda kuma bashi da wasu kwararan hujjoji daya dogara dasu.
Ya kuma ce tuni aka wanke shugaban kasa Tinubu daga zarge-zargen da ake masa, kasancewar makarantar ta tabbatar da cewar shugaban kasar ya yi karatu a cikinta.
Kakakin jam’iyyar APCn na kasa ya baiyana yunkurin da Atikun ke yi a matsayin zafin shan kaye saboda rashin samun zama shugaban kasa.
A wani labarin kuma Ana Fuskantar Barazanar Karancin Man Fetur Da Tashin Farashinsa A Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
