Politics
Babu Ruwan Kwankwaso Da Karar Da Atiku Ya Shigar —Jam’iyyar NNPP
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jam’iyyar NNPP ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar martani da cewa ya daina neman janyo dan takararta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cikin shari’arsa ta kalubalantar zaben nasara Shugaba Tinubu a zabe.
A ranar Alhamis Atiku ya yi taron ’yan jarida inda ya bukaci dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, da kuma Kwankwaso wanda shi ne dan takarar NNPP, su hada kai da shi, wajen fallasa abin da ya kira asirin Tinubu.
Gwamnatin Tinubu Za Ta Binciki Yadda Buhari Ya Tafiyar Da Shirin N-Power
Amma a martanin NNPP a wani taron ’yan jarida a Abuja, Sakaraten jam’iyyar na kasa kuma mukaddashin mataimakin shugaban jam’iyyar, Prince Nwaeze Onu, ya bayyana cewa NNPP ba ta je kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu, don haka ba za ta yi shisshigi ba.
Don haka Atiku da PDP su san inda dare su yi ta kansu, su bar neman janyo NNPP cikin abin da bai shafe ta ba.
A cewarsa, NNPP ta yanke shawarar rashin kalubalantar nasarar Tinubu sabo da kaunar da take wa Najeriya.
A wani labarin kuma Gwamnatin Tinubu Za Ta Binciki Yadda Buhari Ya Tafiyar Da Shirin N-Power
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
